Yadda Donald Trump ya gana da shugaban Syria Ahmed al-Sharaa


Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da sabon shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa, karo na farko cikin shekara 25 da wani shugaban Amurka ya gana da shugaban Syria.

Ganawar shugabannin biyu ta kuma samu halarcin yariman Saudiyya Mohammad Bin Salman wanda ke karɓar baƙuncin Trump a ziyara ta farko da ya kai yankin Gabas ta tsakya tun bayan hawansa kan mulki.

Amurka ta yanke shawarar yin wannan ganawa ce duk da irin damuwa da dari-darin da ake yi da kasancewar sabon shugaban na Syria a matsayin tsohon kwamandan kungiyar AlQaeda.

Wannan ganawa ta shugabannin biyu, ta kasance kari da aka yi daga karshe, bayan tsare-tsaren abubuwan da shugaban na Amurka zai yi a ziyarar da yake yi a Gabas ta Tsakiya da ke zaman babba ta farko bayan ya sake hawa mulki.

 

 

Mista Trump ya sanar da cewa zai cire takunkumin da Amurka ta sanya wa Syria -yana mai cewa da fatan hakan zai iya sa sabuwar gwamnatin za ta iya daidaita al'amuran kasar ta kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Da yake magana a yayin taron habaka dangantaka ta tattalin arziki a babban birnin Saudiyya – Riyadh – Shugaban na Amurka, ya ce takunkumin na Syria wanda yawancinsa an sanya mata shi ne a lokacin mulkin hambarraren shugaban kasar Bashar al Assad, sun cimma burin da aka hara da su – kwalliya ta biya kudin sabulu.


 

Mista Trump ya ce ya dauki wannan matakin ne domin bai wa Syria damar sake habaka.

Ya ce: ''A Syria wadda ta ga akuba da mutuwa – an samu sabuwar gwamnati da ake sa ran za ta samu nasarar sake daidaita kasar ta samar da zaman lafiya . Abin da muke son gani kenan.

A Syria, sun samu kasonsu na kunchi da yaki da kashe-kashe na shekaru masu yawa. Wannan ne dalilin da ya sa tuni gwamnatina ta dauki matakan farko na mayar da dangantaka tsakanin Amurka da Syria a karon farko, a sama da shekara goma.


 

Bayan ganawar ta Trump da sabon shugaban na Syria, shugaban na Amurka daga nan zai hau jirginsa ya nufi Qatar domin wasu karin tarukan a rangadin nasa na gabas ta Tsakiya.

A Qatar din masarautar kasar ta yi masa tayin karrama shi da wani jirgin sama mafi sabunta da kasaita fiye da na shugaban na Amurka wato Air Force One, da zai yi amfani da shi a lokacin ziyarar.

Tayin da ya janyo surutu sosai a Amurka inda jama'a ke cewa shin me shugabannin na Qatar suke nema a dalilin wannan daga Shugaban.