An yi musayar fursunoni tsakanin India da Pakistan
India da Pakistan sun yi musayar fursunoni, kwanaki huɗu bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.
India ta miƙa wa Pakistan wani sojanta da ta kama a farkon watan nan.
Itama Pakistan ta saki wani jami'in sojin India mai tsaron kan iyaka, wanda ya tsallaka yankin Punjab makonni uku da suka wuce.
India ta ce sojan nata ya tsallaka yankin Pakistan ne a ranar 23 ga watan Afirelu, kwana ɗaya kafin harin da ya kashe mutane 25 a yankin Kashmir.
Harin ne kuma ya sa India ta ƙaddamar da nata na ramuwa a kan wasu ƙungiyoyin ƴan bindiga a ɓangaren da Pakistan ke iko da shi a yankin Kashmir.
Ƙasashen biyu sun yi musayar makaman roka kan junan su, kafin daga baya suka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.