Rikicin Indiya da Pakistan kai tsaye: Indiya ta harba makamai masu linzami zuwa Pakistan


Sojojin Indiya sun kaddamar da "Operation Sindoor" - sun kai hari a wurare tara a Pakistan da Jammu da Kashmir karkashin ikon Pakistan.

Rundunar sojin Pakistan ta ce Indiya ta kai wa Pakistan hari da makamai masu linzami a wurare uku kuma Islamabad za ta mayar da martani.

Rundunar sojojin Indiya ta ce a cikin sakon X "an yi adalci" bayan da ta harba makamai masu linzami a cikin yankin Pakistan.

Tashin hankali na kara kamari tsakanin Indiya da Pakistan bayan wani mummunan harin da aka kai a yankin Pahalgam na Kashmir a ranar 22 ga Afrilu.

Popular Posts