Jirgin yakin Amurka na biyu na miliyoyin daloli ya fada cikin tekun Bahar Maliya
Wani jirgin yakin Amurka na miliyoyin daloli ya kasa sauka a kan jirgin Harry S. Truman, ya kuma kutsa cikin tekun Bahar Maliya, kamar yadda kafafen yada labaran Amurka suka rawaito jiya Talata,
Jirgin saman yaki na F/A-18F Super Hornet mai kujeru biyu, wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67, ya nutse a bahar maliya kamar yadda CNN, Wall Street Journal da sauransu suka ruwaito.