Hamas ta sako Ba’Amurke na ƙarshe da ta ke rike da shi a Gaza
Tun farko ƙungiyar Red Cross ce ta tabbatar da cewa mayaƙan Hamas sun miƙa mata Ba’Amurken Edan Alexender a Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, bayan tattaunawar kai tsaye tsakanin ƙungiyar Falasɗinawan da Amurka da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta ƙarbi Alexander tun jiya Litinin, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya miƙa saƙon godiya ga shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya taimaka wajen ganin an sako Alexander.
Sanarwar da ofishin Netanyahu ya fitar ta ce, Firanministan ya tattaunawa ta wayar tarho da shugaba Trump, jim ƙadan bayan sakin Ba’Amurken wanda sojan Isra’ila ne.
Mayaƙan Hamas sun yi wuf da Alexander ne a sansanin soji da ke kudancin Isra'ila a lokacin da suka kai hari har cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023, wanda ya haifar da yaƙin Gaza.
Sakin matashin shine na farko tun bayan da Isra’ila ta rusa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas a watan Maris, inda ta ci gaba da kai munanan hare-hare zirin Gaza, tare da hallaka daruruwan Falasɗinawa.