An yi ruwan bama-bamai a birnin Port na Sudan


 

An kai harin jirage marasa matuka a rana ta uku a jere a birnin Port Sudan na kasar Sudan.

Kafafen watsa labaran kasar sun bayyana cewa an samu munanan fashe-fashe a kusa da babban filin jirgin saman birnin, lamarin da ya sa aka soke tashi da saukar jiragen sama.

Kafafen watsa labaran cikin gida sun ba da rahoton kai hari tashar jiragen ruwa da wasu gine-ginen gwamnati.

An ji tare da ganin fashewar bama-bamai da wuta nan da can a birnin na Port Sudan tun a cikin daren da ya gabata, wanda wannan shi ne kwana na uku a jere da birnin ke shan ruwan bama-bamai da ake kai harin ta hanyar kananan jiragen sama marassa matuka, kamar yadda wasu kafofin watsa labarai na kasar ke bayyanawa.

Sai dai kuma wasu na cewa ba a san sanadin fashewar da tashin wutar ba da kuma ainahin wuraren da hakan ke faruwa a kai, yayin da yakin basasar kasar ya tunkari birnin wanda a da yake shiru daga balahirar yakin.

Rahotannin na cewa an ga hadarin bakin hayaki na tashi daga yankin babbar tashar jirgin ruwan birnin inda dubban mutanen da yakin ya raba da garuruwa da gidajensu suka fake.

Yakin na tsakanin mayakan kungiyar RSF da kuma rundunar sojin kasarta Sudan ya haddasa bala'i mafi muni na jama'a, wanda kuma ake ganin zai ma kara munana a sanadiyyar wadannan hare-hare na birnin na Port Sudan.

Birnin da majalisar dinkin duniya da hukumomi da kungiyoyin agaji har ma da ma'aikatun gwamnatin rundunar sojin kasar suka kafa hedikwatocinsu.

Wannan hari da aka fara kai wa birnin a ranar Lahadi na nuni da kara tsanantar yakin, kasancewar birnin na gabar tekun maliya bai gamu da hare-hare ta kasa ko ma ta sama ba, in banda a wannan makon.

A ranar Lahadi aka kai wani hari da jiragen sama marassa matuka kan wani sansanin soji da ke kusa da babban filin jirgin sama daya kacal da ke aiki a a kasar, bayan wannan harin kuma sai aka kai wasu inda aka hari manyan rumbuna da cibiyoyin adana mai na birnin.


Popular Posts