Shugabannin Koriya ta Kudu sun nemi kwanciyar hankali bayan tsige Shugaba Yoon
Koriya ta Kudu na yunkurin sake tabbatar da kawayenta yayin da madugun 'yan adawar kasar ya yi tayin yin aiki da gwamnati, a wani yunƙuri na maido da kwanciyar hankali bayan tsige shugaba Yoon Suk-yeol.
Mukaddashin shugaban kasar Han Duck-soo ya tattauna da shugaban Amurka Joe Biden ta wayar tarho ranar Lahadi, fadar White House da ofishin Han sun ce, kwana guda bayan da aka dakatar da Yoon saboda yunkurin kafa dokar soji a farkon wannan watan.
Majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta kada kuri'a a ranar Asabar don tsige Yoon tare da dakatar da shi daga aikinsa, bayan da ya jefa Koriya ta Kudu cikin rudanin siyasa tare da kwace ikonsa.
Han, wanda ke rike da mukamin firaminista bayan da Yoon mai ra'ayin rikau ya zabe shi, an daukaka shi zuwa mukaddashin shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, yayin da shari'ar Yoon ta koma kotun tsarin mulkin kasar.
"Koriya ta Kudu za ta aiwatar da manufofinta na harkokin waje da na tsaro ba tare da tsangwama ba, kuma za ta yi kokarin tabbatar da kiyaye kawancen Koriya ta Kudu da Amurka da kuma ci gabanta," in ji Han, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa.