Rasha ta kusa cimma muradin ta a yaƙin Ukraine - Putin


Shugaba Putin ya ce dakarun Rasha sun kama hanyar cimma nasara a yaƙin da suke da Ukraine.

Da ya ke jawabi a wajen taron da ya saba yi kowacce shekara, Mista Putin ya ce dakarunsa suna ci gaba da mamaye muhimman wurare a Ukraine.

Amma bai bayyana haƙiƙanin kusancin da Rasha ta kai ga cimma muradin ta na yaƙin ba.

Shugaban Rashan ya kuma bayyana aniyar sa ta ganawa da Donald Trump a duk lokacin da zaɓabben shugaban Amurkan ya shirya.

Ya kuma yi iƙirarin cewa tattalin arzikin Rasha yana bunƙasa cikin sauri fiye da na Amurka da kuma tarayyar Turai.