Skip to main content
NSCDC ta ce ta gano wurin ɓoye ɗanyen mai da ake sacewa a Ribas
Hukumar tabbatar da tsaro da kare hakkin al'umma ta Civil Defense ta ce ta gano wani gida da ake ɓoye haramtaccen mai a jihar Ribas.
Gidan wanda ke karamar hukumar Obio/Akpo na jihar, an gano yana ɗauke da tankokin ajiya da dama da kuma jarakuna, cike da ɗanyen mai da aka sato.
Kwamandan hukumar ta Civil Defense a jihar, Joachim Okafor wanda ya jagoranci tawagar hukumar zuwa wurin, ya bayyana cewa sun samu nasarar gano wurin ta hanyar amfani da wata fasaha da ke bin diddigin irin waɗannan wurare da ake ajiye haramtaccen mai.
Okafor ya ce ayyukan masu satar ɗanyen mai, na janyo babban barazana ga muhalli da kuma lafiyar al'ummar.