Me ya sa gwamnonin Najeriya ke son kafa ƴansandan jihohi?


Yadda gwamnonin Najeriya ke ta nanata buƙatar samar da 'yansandan jiha domin magance matsalolin da suke fuskanta a jihohinsu ya sa wasu na tambayar me ya sa suka haƙiƙance.

A ranar Alhamis ne gwamnan Kaduna da ke arewacin Najeriya, Uba Sani, ya ce gwamnoni da dama sun nuna goyon bayansu kan buƙatar samar da ƴansandan na jihohi saboda yanayin matsalolin tsaro da ake fama da su a jihohi.

Sai dai ya ce majalisar ta ɗage tattaunawar zuwa watan Janairun 2025.

Batun ƴansandan jihohi na cikin abubuwan da aka daɗe ana muhawara kansu a Najeriya, inda wasu ƴansiyasa ke amfani da shi wajen kamfe a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Sai dai wasu na zargin gwamnoni za su iya amfani da ƴansandan na jihohi domin takawa tare da cin mutuncin abokan hamayyarsu na siyasa, da kuma wuce gona da iri wurin gudanar da harkokinsu. Sai dai sun sha musanta zargin.

Magance matsalar tsaro
Gwamnoni da dama na bayyana cewa me ɗaki shi ya san inda ruwa yake zuba, inda suke amfani da irin wannan bayanin domin gamsar da mutane buƙatar da suke da ita ta samun ƴansandan jihohi.

Jim kaɗan bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Gwamna Uba Sani ya yi wa mane labarai bayanin abin da suka tattauna.

"Duka jihohi 36 sun miƙa martaninsu da aka ce su kawo kan maganar ƙirƙiro ƴansandan jihohi. Kusan dukkan jihohin sun yarda cewa ƴansandan jihohi ne za su kawo ƙarshen wannan matsala da ake fama da ita ta matsalar tsaro."

A cewarsa, akwai aƙalla mutum miliyan 230 a Najeriya, yayin da ƴansandan ƙasar ba su wuce 230,000 ba.

"Akwai wurare a ƙasar nan da sai ka yi tafiyar kilomita 30 zuwa 100 ba ka ga jami'an tsaro ba."

Sai dai Group Captain Sadiq Garba Shehu (mai ritaya), wani mai sharhi kan harkokin tsaro, ya ce yana ganin zai fi kyau gwamnatin taryya ta ɗauki ƙarin ma'aikata maimakon ƙirƙirar 'yansandan jihohi.

Amfani da manyan makamai
Wani batun da yake jan hankalin mutane shi ne amfani da manyan makamai irin su bindiga ƙirar AK-47 da ƴanbindiga ke yi.

Sai dai dokokin Najeriya ba su yarda mutumin da ba jami'in tsaro ba ya riƙe babban makami ba kamar AK-47. Gwamna Uba Sani ya ce hakan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa suke neman rundunar 'yansandan.

"Shi ya sa (dokar) samar da ƴansandan na jihohi zai ba su dama su riƙe makamai irin su AK47. Doka ba ta bai wa ƴan sa-kai damar riƙe manyan makamai ba, kuma idan ka ga irin makaman da ƴanta'addan suke riƙewa akwai matsala," a cewarsa.

Captain Sadiq Garba ya shaida wa BBC cewa su kansu ƴan sa-kai ɗin da suke amfani da bindiga babu wata dokar da ta ba su dama.

"Idan aka duba, za a ga suma ƴan sa-kai ɗin babu wani takamamaiman lokacin da aka ba su izini. Kuma in ka zagaya wasu jihohi za ka ga suna amfani da bindigar farauta, wasu kuma da sanda ko gora.

"A jihar Borno aka fara maganar ƴan sa-kai ɗin. Da farko a hankali suka fara, lokacin ba su da bindiga, daga baya suka fara amfani da bindiga. Kuma gaskiya da wahala ka iya gano lokacin da gwamnati ta ce su yi hakan."

Ya ƙara da cewa su ma ƴan sa-kai ɗin an samu wuraren da aka zarge su da cin mutuncin mutane, da zargin kisan gilla a wasu jihohin.

"A maganar bindiga kuma, akwai dokar amfani da manyan bindigogi da ta ce dole sojoji ko ƴansanda na tarayya ne kaɗai za su yi amfani da su. Gaskiya idan aka sakar musu mara akwai matsala," in ji shi.

Sanin lungu da saƙo
Haka kuma Gwamna Uba Sani ya ce samun ƴansandan na jihohi zai taimaka saboda su ne suka san lungu da saƙon jihohin da suke.

A cewarsa: "Idan ka ɗauki ɗansanda ɗan Birnin Gwari (a Kaduna), za ka ga ya san dazukan yankin sosai, ya san lungu da saƙo, kuma ya san kowa a wurin."

Yayin wata tattaunawa da BBC lokaacin da aka sace ɗaliban makarantar Kuriga a jihar Kaduna, Uba Sani ya faɗa wa cewa a kundin tsarin mulkin, ba za su iya gina ofishin ƴansanda ba sai sun samu izini wajen shugaban ƴansanda.

Mece ce fargabar?
Sai dai mutanen gari suna nuna fargabar amfani da ƴansandan na jihohi ka iya kaiwa ga muzguna wa abokan hamayya.

Group Captain Sadiq ya amince da hakan yana mai bayar da shawarar ƙara yawan 'yansandan tarayya.

"Wannan magana ta taso ne saboda yadda gwamntin tarayya ta kasa samar da isassun ƴansanda.

"Ni shawarata ita ce gwamnatin tarayya ta ɗauki ƙarin ƴansandan saboda muna da matasa ƙarfafa. Idan ka ce kana neman ƴansanda 20, za ka samu maza majiya ƙarfi sun fi 5,000 suna nema. Haka ma soja."

Ko me ya sa yake shakkar bai wa jihohi wannan dama?

"Ko a cikin kwanakin nan an ji wurare daban-daban da gwamnoni suka sa aka kama wasu. Wannan fa da ƴansandan tarayya ne. Idan aka sakar musu mara, za a samu matsala."

Popular Posts