Masar ta ƙaddamar da sabuwar tashar lantarki mai ƙarfin megawatts 500


Masar ta kaddamar da wata tasar samar da lantarki na hasken rana wanda aka kashe dalar Amurka miliyan 500 a birnin Aswan da ke kudancin kasar a ranar Asabar.

Wannan na cikin ƙoƙarin da ƙasar ke yi na bunkasa samar da makamashin da ake iya sabuntawa bayan da aka yi fama da matsalar wutar lantarki a kwanakin baya a ƙasar.

Tashar ta Abydos Solar PV Plant, wanda kamfanin samar da makamashi na kasar Dubai AMEA Power ya samar, yana da karfin megawatts 500 kuma an kammala shi cikin watanni 18 kacal.

Ana sa ran tashar lantarkin za ta samar da tsaftataccen makamashi gigawatt-hours 1,500 a duk shekara, wanda zai iya samar da wutar lantarki ga kusan gidaje 300,000, wanda hakan zai kawar da tan 782,300 na hayaƙi mai gurɓata muhalli na CO2, a cewar AMEA Power.

Aikin wani muhimmin mataki ne na bunkasa amfani da makamashin da ake sabuntawa a Masar, kuma wani bangare ne na "dabarun kasa da nufin rage dogaro da hanyoyin samar da makamashi na gargajiya", in ji Firaminista Minista Moustafa Madbouly yayin bikin kaddamar da kamfanin a ranar Asabar.

Firaministan ya kuma bayyana cewa wannan aikin zai kuma taimaka wa gwamnati a yunƙurin da take yi na daƙile yawan ɗaukewar wutar lantarki wanda ya zama ruwan dare musamman a lokutan da ake cikin tsanananin buƙatar lantarkin.


Popular Posts