Majinyata 60 a asibitin Gaza na fuskantar barazanar yunwa, in ji hukumomi lafiya
Majinyata da dama da suka jikkata a asibitin Indonesiya da ke arewacin Gaza da Isra'ila ta yi wa kawanya na cikin hadarin mutuwa sakamakon rashin abinci da ruwan sha, in ji hukumomin kiwon lafiyar Falasdinu.
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta fada a yammacin ranar Talata cewa marasa lafiya 60 na cikin "hadarin mutuwa".
"Yanayin jin kai a cikin asibitin ya zama mai matukar hadari, saboda wadanda suka jikkata ba su da bukatu na yau da kullun, wanda ke kara musu wahala a cikin mawuyacin hali da sojojin [Isra'ila] suka sanya," in ji ma'aikatar cikin wata sanarwa.
Asibitin yana a Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza, wanda ke karkashin wani tsauraran matakan tsaro na sojojin Isra'ila tun farkon watan Oktoba.
A cikin bayananta na daban na yau da kullun kan adadin mutanen da suka mutu a yakin Isra'ila a Gaza, ma'aikatar ta ce akalla mutane 28 ne suka mutu tare da jikkata wasu 54 a "kisan gilla guda hudu kan iyalai" a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Ma'aikatar ta kara da cewa "Da yawan wadanda abin ya shafa har yanzu suna karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, kuma motar daukar marasa lafiya da jami'an tsaron farar hula ba za su iya isa gare su ba."