Majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta kada kuri'ar tsige shugaba Yoon Suk-yeol

Wasu mambobin jam'iyyar Yoon ta masu ra'ayin mazan jiya ta People Power Party sun ba da muhimmiyar kuri'un da ke goyon bayan tsigewar.

 

Dubun dubatar masu zanga-zangar ne suka shiga wani maci a birnin Seoul inda suke kira da a tsige shugaban Koriya ta Kudu daga mukaminsa tare da kama shi sakamakon ayyana dokar ta-baci na tsawon lokaci.

Majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol sakamakon wani dan gajeren lokaci da ya yi na kokarin kafa dokar soji, matakin da ya jefa Koriya ta Kudu cikin rudanin siyasa a rabin shugabancinsa.

Majalisar wakilai ta kasa ta kada kuri'a 204 zuwa 85 ranar Asabar don tsige Yoon, kuri'a na biyu cikin kwanaki takwas.  Mambobi uku ne suka ki kada kuri’a, sannan aka bayyana kuri’u takwas ba su da inganci.

An gudanar da zaben ne ta hanyar jefa kuri'a a asirce, inda kashi biyu bisa uku na kuri'un da ake bukata domin tsige shugaban.  Dukkan ‘yan majalisar 300 ne suka kada kuri’unsu.

An ji hayaniya mai zafi daga zauren majalisar yayin da aka bayyana sakamakon zaben.  A waje, dubban masu zanga-zangar ne suka tarbi sanarwar da tafi da kakkausar sowa.

Rob McBride na Al Jazeera, yana ba da rahoto daga cikin ginin majalisar, ya bayyana yanayin a matsayin "sausanci" bayan kada kuri'ar.

Sai dai wakilinmu ya ce har yanzu rigingimun siyasa ba su kare ba saboda shugaban ya sha alwashin yaki” karar tasa a gaban kotu.

Popular Posts