Majalisar dattijan Philippines ta amince da sabuwar yarjejeniyar tsaro da Japan


Kasar Philippines ta amince da sabuwar yarjejeniyar tsaro da kasar Japan wadda za ta bai wa sojojin kowace kasa damar girke a kasarsu a daidai lokacin da ake kara takun saka tsakaninta da kasar Sin.

Majalisar dattijan Philippines ta sanar da amincewar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, tana mai cewa "zai inganta hadin gwiwa" tsakanin sojojin Japan da Philippines.

Amincewa da yarjejeniyar yana kara tabbatar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu da kuma burinsu na kara ba da gudummawa ga zaman lafiya da tsaro a shiyya-shiyya da na kasa da kasa,” inji Majalisar Dattawan kasar.

Jakadan Japan a Manila, Kazuya Endo, ya halarci taron zartar da yarjejeniyar.

Endo ya yi maraba da kammala yarjejeniyar a cikin wata sanarwa da ta yada a shafukan sada zumunta, yana mai cewa yana fatan za ta “za su aiwatar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin sojojin kasashen biyu, da kara inganta hadin gwiwar  tsaro, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasashen biyu.  Yankin Indo-Pacific".