Lamine Yamal zai yi jinyar mako huɗu sakamakon rauni


Bayan kashin da ta sha a hannun Leganes ranar Lahadi har gida, Barcelona na fuskantar matsalar rashin zaƙaƙurin ɗanwasa Lamine Yamal sakamakon raunin da ya ji a idon sawunsa.

An yi wa ɗan ƙwallon mai shekara 17 gwaji a safiyar Litinin domin sanin halin da yake ciki bayan ƙetar da Neyou ya yi masa a wasan na ranar Lahadi, kuma sakamakon ya nuna rauni a idon sawunsa na dama.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ɗan ƙasar Sifaniyan zai yi jinyar mako uku zuwa huɗu.

A watan Nuwamba ma ɗanwasan ya yi jinya bayan ya ji rauni a idon sawun nasa yayin wasan Champions League da Red Star, wanda ya kai shi ga yin jinyar kusan mako uku.

Yayin wasan na Leganes a filin wasa na Camp Nou, minti 15 da fara wasa ne Neyou ya murƙushe Lamine. Duk da cewa ya ci gaba da wasan har zuwa minti na 74, an ga yadda ya kasa taɓuka komai saboda raunin.

Jinyar za ta sa ɗanwasan ba zai buga wasan La Liga na hamayya tsakaninsu da Atlético Madrid ba ranar Asabar mai zuwa. Kazalika akwai wasan Copa del Rey da kulob ɗin Barbastro ranar 4 ga watan Janairu.

Haka nan, babu tabbas ko zai buga wasan gab da ƙarshe ba na gasar Spanish Super Cup wanda za su gwabza da Athletic Bilbao ranar 8 ga watan Janairu.

Yamal ya ci wa Barcelona ƙwallo biyar a gasar La Liga ta bana, sannan ya bayar aka ci tara.