Kasashen Larabawa takwas sun sha alwashin tallafawa ‘tsarin mika mulki cikin lumana’ a Syria


Manyan jami’an diflomasiyya daga kasashen kungiyar Larabawa takwas sun amince a wani taro a kasar Jordan don “goyon bayan tsarin mika mulki cikin lumana” a Syria bayan hambarar da shugaba Bashar al-Assad.

Ministocin harkokin wajen kasashen Jordan, Saudiyya, Iraki, Lebanon, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Qatar sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a jiya Asabar bayan da suka gana a tashar ruwa ta Aqaba ta gabar tekun Jordan.

Sun ce "dukkan dakarun siyasa da na zamantakewa" dole ne su kasance da wakilci a cikin sabuwar gwamnatin Siriya kuma sun yi gargadi game da "duk wata kabila, bangaranci ko addini" tare da yin kira ga "adalci da daidaito ga dukkan 'yan ƙasa".

Sanarwar ta ce, ya kamata tsarin siyasa a kasar Syria ya goyi bayan "Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan Larabawa, bisa ka'idar kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2254", wani kuduri a shekarar 2015 wanda ya tsara taswirar sasantawa.

Jami'an diflomasiyyar Larabawa sun kuma halarci wani taro na daban a birnin Aqaba wanda ya hada da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, da jakadan MDD na musamman kan Syria Geir Pederson da jami'in harkokin wajen kungiyar EU Kaja Kalas, da ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan.

Popular Posts