Hedikwatar tsaro ta musanta kafa sansanin sojin Faransa a Najeriya


Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce babu gaskiya a labaran da ake yaɗawa cewa dakarun Faransa na shirin kafa sansaninsu a Najeriya.

Wata sanarwar da daraktan yaɗa labaran Hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce labaran jita-jita ce, kuma basu da tushe.

Ya ce, “An ankarar da hedikwatar tsaron Najeriya a kan rahotannin da ake yaɗawa a shafuka sada zumunta da ke zargin cewa zangon farko na dakarun Faransa ya isoa Maiduguri a shirye-shirye kafa sansanin su a yanki Arewa maso gabashin Najeriya.

“Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa wannan rahoto na ƙarya ne kuma bashi da makama. Idan za a iya tunawa babban hafsan Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi bayani game da wannan batu, kuma ya jaddada cewa jita-jita ne kawai aka kitsa a wannan labari.''

Hedikwatar tsaron ta buƙaci jama'a su yi watsi da rahotannin ƙaryar, waɗanda ta ce har yanzu akwai masu ci gaba da yaɗa su domin cimma muradun su na son rai.


Popular Posts