Hada-hadar naira miliyan 1.2 kawai masu PoS za su yi a rana - CBN


Babban bankin Najeriya CBN ya taƙaita hada-hadar kuɗin da masu PoS za su yi a rana zuwa naira miliyan 1.2.

Wannan umarnin na ƙunshi ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Talata game da taƙaita hada-hadar kuɗi ga wakilan bankuna.

"Bankin ya ɗauki wannan matakin ne domin ƙara jawo hankalin masu hada-hadar kuɗi zuwa ga rage amfani da tsabar kuɗi," kamar yadda sanarwar, wadda Oladimeji Yisa Taiwo ya sa hannu a madadin daraktan tsare-tsaren fitar da kuɗi.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa kwastoma ba zai cire sama da naira 500,000 ba a mako.