Gwamnonin Najeriya sun yi taro a 'kan dokar haraji'


 

Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta yi wani taro a cikin dare a hedikwatarta da ke birnin Abuja, inda rahotanni ke cewa sun tattauna abubuwa da dama ciki har da batun ƙudirin dokar haraji da ta janyo cece-ku-ce a ƙasar.

Babu dai bayani daga gwamnonin a kan abin da taron nasu ya cimma wa, amma rahotanni daga jaridun ƙasar sun ce batun ƙudirin dokar harajin ne jigo a zaman gwamnonin na jiya Laraba da daddare.

Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki ne suka fi yawa a taron, inda aƙalla 15 suka halarta, sai gwamnoni biyu daga jam'iyyar Labour da kuma na APGA ɗaya.

Ƙudirin dokar harajin wanda shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar ya janyo suka da ƙorafi daga masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnonin ƙasar a ƙarƙashin majalisar ƙoli ta tattalin arziki, da gwamnoni da ƴan majalisa daga yankin arewa da ma ƙungiyoyi da dama.

Gwamnonin Arewa 19 kuma sun bayyana rashin goyon bayan su ga wasu sassa na ƙudirin, tare da neman a gaggauta janye shi daga majalisar dokokin tarayya.


Popular Posts