Ƴanbindiga sun kashe sojojin Nijar fiye da 90
Wani mummanan hari da ake zargi ƴanbindiga ne suka kai ya yi sanadiyar kashe sojojin Jamhuriyar Nijar sama da 90 da fararen hula fiye da 40.
Wasu majiyoyi daga ƙasar sun ce ƴanbindigar sun kai hare-hare ne a ƙauyen Chatoumane, da Anzourou a lokaci guda dukkansu a yankin Tillaberi.
A ɗaya daga cikin hare-haren da ake tunanin ya fi muni, ƴanbindigar, waɗanda suka saje da fararen hula sun buɗe wuta kan sojoji a kasuwar ƙauyen Chatoumane, amma kuma sojoji ba su samu damar mayar da wutar ba saboda gudun kashe waɗanda babu ruwansu.
Wasu majiyoyi daga ƙasar sun ce an kashe sojoji 91 da fararen hula 43 - amma ana tunanin har da ƴanbindigar a ciki.
Har yanzu hukumomi a ƙasar ba su ce komai ba game da hare-haren.
A watan Yunin da ya gabata, an kashe aƙalla sojoji da fararen hula 20 a wasu hare-hare da ƴanbindigar suka kai a kusa da iyakar ƙasar da Burkina Faso.
Nijar ta haɗa alaƙar tsaro da Mali da Burkina Faso ne bayan ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma wato Ecowas.