Yakin Rasha da Ukraine: Harin kan iyaka ya tsananta bayan da Putin ya sake lashe zabensa
Wani ma'aikacin kashe gobara ya kashe wuta a cikin wata mota da ta lalace yayin harin makami mai linzami da Rasha ta kai a Mykolaiv, Ukraine |
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce kasarsa ba za ta ji tsoro ba yayin da yake tabbatar da kamun ludayinsa a zaben da aka yi.
Kawayenta irin su China sun yi gaggawar taya Putin murna amma kasashen yamma sun yi tir da abin da suka kira zaben da ya saba wa doka.
Ukraine ta ce ana kwashe mazauna yankunan kan iyaka a yankin Sumy da ke arewa maso gabashin kasar saboda karuwar hare-haren da Rasha ke kaiwa.
Rasha ta yi ikirarin harbo makaman roka na Vampire 8, Alder biyu da kuma Grad daya harba makamin roka a yankin Belgorod.