Rasha-Ukraine: Rasha ta ce ta kwace kauyen Orlivka


 

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kwace kauyen Orlivka da ke yankin gabashin Donetsk na kasar Ukraine mai tazarar kilomita 9.5 daga garin Avdiivka da ke karkashin ikon Rasha.

Moldova ta kori jami'in diflomasiyyar Rasha saboda bude rumfunan zabe na zaben shugaban kasar Rasha a yankin da ya balle na Transnistria, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar bayan kiran jakadan na Rasha.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya habarta cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai tafi kasar China a watan Mayu domin tattaunawa da takwaransa na China Xi Jinping.

Babban kwamandan sojojin Ukraine Oleksandr Syrskii ya ce ci gaban tsarin da ba a sarrafa ba, ko jirage marasa matuka, yana da mahimmanci wajen bai wa Kyiv wata fa'ida akan sojojin Rasha "mafi girma".

Popular Posts