Rahotanni daga birnin Moscow na kasar Rasha sun ce akalla mutane 133 sun mutu, sama da 100 kuma suka jikkata
Kungiyar ISIS-K (ISIL) ta dauki alhakin kai wani mummunan hari da aka kai a dakin taro na Crocus City Hall na Moscow wanda ya kashe akalla mutane 133 tare da raunata fiye da 100.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Rasha ta ce 'yan bindiga hudu da ake tsare da su 'yan kasashen waje ne. An kama mutane 11 da ke da hannu a harin.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da mummunan harin ta'addanci da aka kai a Krasnogorsk.