Putin ya yi iƙirarin lashe zaɓen Rasha a karo na biyar
Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce nasararsa a zaɓen shugaban kasar ta nuna karara yarda mutane ke kaunar muradansa.
A jawabin da ya gabatar bayan sakamakon zaɓe ya nuna ya samu kusan kashi 90 cikin100 na kuri'un da aka kada, Mista Putin ya ce idan 'yan Rasha suka haɗa kansu babu wanda ya isa ya yi musu barazana ko dannesu.
Kusan a bayyana yake cewa Vladimir Putin zai yi ikirarin nasara a karo na biyar na wannan zaɓe da gagarumin rinjaye, duk da cewa ya fuskanci adawa daga 'yan takara uku da ake yiwa kallon 'yan koren gwamnatin Kremlin.
Sai dai Jami'an zaɓe na sanar da cewa ya samu sama da kashi 87 na kuri'un da aka kada, sai gashi ya fito yana cewa dimokuradiyar Rasha tafi ta kasashen yammanci sahihanci.
A tsokacinsa kan yaƙin Ukraine, ya ce abin da zai bai wa fifiko a yanzu shine sake karfafa sojojin Rasha. Ya kuma ce sojojinsa jajirtatu ne a fagen yaƙi da Ukraine.
Ya ce "A takaice dai, sannin kowa ne cewa sojojinmu akwai jajircewa. A yankuna da dama mazanmu su yi gunduwa-gunduwa da makiyanmu".
"Kullum sake nausawa muke yi. Sannu a hankali, cikin hikima, kuma a koda yaushe. Wannan ya zarta batun kare kai kaɗai. Salonmu ya sha bamban".
ABINDA DUNIYA KE CEWA
Kasahen duniya da dama dai sun yi alla-wadai da zaɓen Rasha da suke bayyanawa da tamkar wani shirin fim.
Amurka ta ce kwata-kwata babu batun sahihanci ko adalci a zaɓen, tare da tunasar da cewa Putin ya garkame abokan hamayyarsa na siyasa, da kuma datse sauran daga shiga takara.
Haka ita ma Poland ta yi irin wadannan zarge-zarge na tauye yancin dimokuradiya.
Sai dai shugaban Venezule, Nicolas Maduro, ya yi murna da nasarar Vladimir Putin.
Ya ce tabbas Putin ya yi nasara a yaƙinsa shi ɗaya tilo da ilahirin ƙasashen yamma da suka haɗe masa kai.
"Wannan na sake fito da martaba da akidun al'ummar Rasha wanda hakan ya kai ga wannan nasara ta Shugaba Vladimir Putin".
"Wannan nasara na sake buɗe sabon babin rayuwa a Rasha a wannan duniya na taron dangi. Don haka ɗan uwanmu, Vladimir Putin ya basu kunya da nasararsa".
Shugaba Zelensky na Ukraine, ya ce wannan salon zaɓe na sake nuna karara cewa Putin ba zai hakura ba, haka zai ta mulki har abada.
Zelensky ya ce har a yankunasu da Rasha ta mamaye aka yi wannan zaɓe mara halasci.