Kotun Indiya ta haramta makarantun addinin Musulunci a jihar Uttar Pradesh gabanin zaɓe
Haramcin da aka sanya wa makarantun addinin Musulunci na iya shafar dalibai miliyan 2.7 da malamai 10,000, a cewar Shugaban Hukumar Makarantu.
Gwamnatin jihar Uttar Pradesh ta dakatar da shirin bayar da tallafi ga makarantun addinin musulmi a watan Janairu, lamarin da ya sa malamai 21,000 suka rasa aikin yi.
Wata kotu a ƙasar Indiya ta sanya dokar haramta makarantun addinin Musulunci a jihar Uttar Pradesh wadda ke da mafi yawan al'umma a kasar.
Matakin da aka dauka ka iya ƙara nisantar da al'ummar Musulmai da dama daga gwamnatin Hindu mai kishin ƙasa ta Firaminista Narendra Modi, gabanin zaɓen kasar da ke tafe.
Hukuncin da aka yanke a makon da ya gabata ya yi watsi da dokar da aka kafa a shekarar 2004 da ke kula da makarantun addini na Musulunci a Uttar Pradesh, yana mai cewa an saɓa wa tsarin mulkin kasar Indiya tare da ba da umarnin a mayar da dalibai zuwa koyarwar makarantun zamani.
Umarnin Babbar Kotun Allahabad ya shafi dalibai miliyan 2.7 da malamai 10,000 na makarantun addini 25,000, a cewar Iftikhar Ahmed Javed, shugaban hukumar ilimin addinin gargajiya a jihar, inda kashi biyar na al'ummar jihar mutum miliyan 240 Musulmai ne.
''Gwamnatin jihar za ta kuma tabbatar da cewa, a bar yaran da ke tsakanin shekaru shida zuwa 14 ba tare da an basu damar shiga waɗannan cibiyoyi da aka ware ba,'' a cewar takardar umarnin da alkalai Vidyarthi da Vivek Chaudhary suka sanya wa hannu, wanda ya biyo bayan ƙarar da lauya Anshuman Singh Rathore ya gabatar.
Sai dai ba a samu damar tantance ko Rathore na da alaƙa da wata ƙungiyar siyasa ba.
Ayyukan nuna wariya
Indiya za ta gudanar da babban zaben kasar a tsakanin watan Afrilu da Yuni wanda ake sa ran jam'iyyar Bharatiya Janata ta Modi (BJP) za ta yi nasara.
Musulmai da kungiyoyin kare hakkin ɗa'nadam sun zargi wasu mambobin kungiyar BJP da yada kalaman nuna kyamar musulmai da tsangwama da kuma rusa kadarori na Musulmai.
Modi dai ya musanta cewa ana nuna bambancin addini a Indiya.
BJP ta ce gwamnati na gyara kura-kuran tarihi da aka yi gadon su, ciki har da wani gidan ibada na Hindu da aka ƙaddamar a daɗɗaɗen wuri da aka taɓa gina wani masallaci tun a ƙarni na 16 wanda aka lalata shi a shekarar 1992.
Yawancin mabiya addinin Hindu sun yi imanin cewa an gina masallacin ne inda aka haifi Ubangijinsu Sarki Ram da kuma rushe waurin ibada da aka yi karkashin mulkin Sarkin Mughal Babur.
Rakesh Tripathi, mai magana da yawun jam'iyyar BJP a Uttar Pradesh, kana wanda ke tafiyar da harkokin gwamnatin jihar, ya ce ba a yi hakan don adawa ko saɓa wa makarantun addinin Musulunci ba ne, amma nuna damuwa ga karatun dalibai Musulmai.
"Ba ma adawa da kowace makarantar addini (Madarasah) amma muna adawa da ayyukan nuna wariya, muna adawa da bayar da kudade ba bisa ka'ida ba, kuma gwamnati za ta yanke hukunci kan wasu matakai bayan ta bi umarnin kotu."
Ofishin Modi bai ba da amsa kai tsaye ga sakon imel da ke neman sharhi kan hukuncin kotun ba.
Daidaita ayyuka
Jami'in makarantar addini Javed, wanda kuma shi ne sakataren kasa na reshen marasa rinjaye na jam'iyyar BJP, ya ce a matsayinsa na Musulmi sau tari da dama yakan shiga tsaka-mai-wuya wajen goyon bayan jam'iyyarsa da kuma ƴan'uwansa Musulmai.
Ya ce tun bayan wannan umarni na Kotu ya ke ta samun kiraye-kiraye daga ‘yan'uwa Musulmai, lamarin da ya faru cikin watan Ramadan mai alfarma.
"Wasu lokutan, abubuwa sukan rincaɓe," in ji shi.
“Dole ne na yi ƙoƙarin daidaita abubuwa, a matsayina na Musulmi jam’iyya ta tura ni zuwa ga al’umma domin in shawo kan su su zabe mu, su kuma shiga jam’iyyar, ina jin tsoro kuma ina tafiya da jami'an tsaro a duk lokacin da zan je wani taron jama’a ko wani shiri."
Tripathi na jam'iyyar ya mayar da martani da cewa shugabannin BJP Musulmai ba su da wani dalili na jin tsoro saboda al'ummarsu suma suna cin moriyar shirye-shiryen gwamnati daban-daban da ake yi.
"Ni Hindu ne kuma ina yawan ziyartar al'ummar Musulmai kuma ina samun goyon baya mai kyau daga gare su," in ji shi.
"Gaskiyar maganar ita ce jam'iyyar BJP da gwamnati sun himmantu wajen samar da ilimi da kuna suna iya kokarinsu wajen cimma hakan.''
Kungiyar dattawa ta BJP ta yi ta dora Musulmai masu biyayya zuwa ga matsayin jagoranci a jami'o'in Musulunci a Indiya a wani mataki na samun kuri'un musulmai gabanin zaben kasar.
Gwamnatin Uttar Pradesh ta dakatar da shirin bayar da tallafi ga makarantun addinin Musulunci a watan Janairu, lamarin da ya sa malamai 21,000 suka rasa aikin yi.
Umurnin na ranar Juma’a ya shafi dukkan makarantun addinin musulunci da ke jihar, masu zaman kansu da na gwamnati, in ji Javed.
Kotun dai ba ta ba da wani takamaiman lokaci da umarnin nata zai soma aiki ba, amma Javed ya ce da wuya a iya rufe makarantun addinin Musulmi nan take.