Gwamnan Kano bai ji dadin yadda ake raba abincin buda baki ba

 


Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin ransa kan yadda ake gudanar da aikin shirin raba abincin azumi da ake yi a jihar.


Yayin wata ziyarar bazata da ya kai ɗaya daga cibiyoyin da ake aikin raba abincin a Ƙaramar Hukumar Municipal, gwamnan ya nuna rashin jin dadi game da irin abincin da ya gani ana rabawa a cibiyar.

Alala ce da farar shinkafa da manja, inda ya rika tambayar yaran da aka rabawa cewa "manja suke samu ku ba miya ba?".

Gwamnan ya koka kan yawa da kuma ingancin abinci da ya ga ana rabawa, wanda a cewarsa ya sha banban da abin da gwamnainsa ta amince ta kuma sahale a rika rabawa.

"Wannan wane irin shirme ne," in ji gwamnan lokacin da yake zantawa da masu dafa abincin, yana tambayarsu wanene ya ba su damar dafa abincin a wannan tsari.

Abba ya ja kunnan masu dafawar tare da ba su sako su shaidawa waɗanda suka ba su damar aikin, cewa kada ya sake dawowa ya tarar da irin wannan abincin da hankalinsa bai kwanta da shi ba.


Popular Posts