Akalla gawarwakin mutane 12 ne aka gano bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin Haiti
'Yan sanda sun yi sintiri a Port-au-Prince, Haiti, bayan da hukumomi suka tsawaita dokar ta-baci |
Akalla gawarwakin mutane 12 ne motar daukar marasa lafiya ta kwashe daga unguwar masu hannu da shuni na Petion-Ville da ke wajen babban birnin kasar Haiti Port-au-Prince, yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula har zuwa lokacin da za a sanar da sabuwar gwamnati.
Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mutane a yankunan tsaunuka na Laboule da Thomassin kafin fitowar rana a ranar Litinin, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin tserewa kamar yadda wasu suka kira gidajen rediyo suna rokon ‘yan sanda.
Mazauna wajan sun kasance cikin kwanciyar hankali duk da yawaitar hare-haren gungun 'yan bindiga a duk fadin Port-au-Prince da suka fara a ranar 29 ga Fabrairu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters da Associated Press sun ruwaito cewa, an kwashe gawarwakin mutanen da aka harba daga babbar hanyar da ta shiga cikin unguwar da kuma wajen wani gidan mai.
Hare-haren na baya-bayan nan sun haifar da fargabar cewa ba za a kawo karshen tashin hankalin kungiyoyin ba, duk da cewa Firayim Minista Ariel Henry ya sanar kusan mako guda da ya gabata cewa zai yi murabus da zarar an kafa majalisar shugaban kasa ta rikon kwarya. Majalisar za ta samu wakilai bakwai da za su kada kuri’a da masu sa ido biyu daga kungiyoyin kawancen siyasa da sassan al’umma daban-daban.
Shugabannin kungiyoyin, wadanda suka dade suna neman tsige Henry, sun yi gargadin "yaki" ga Haiti tare da yin barazana ga 'yan siyasar da suka shiga majalisar mika mulki. A halin da ake ciki, mazauna garin na fuskantar matsalar karancin abinci da kuma kula da lafiya.
Haiti dai na fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru da suka kai ga mafi muni bayan kashe shugaba Jovenel Moise a shekarar 2021.