Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Houthi ba ta hada da Isra'ila, ba in ji kakakin Houthi
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin 'yan Houthi na Yemen da Amurka ba ta hada da kare Isra'ila daga ayyukanta ba, in ji kungiyar a ranar Laraba, tana mai nuni da cewa hare-haren jiragen ruwa da ke kawo cikas ga harkokin kasuwancin duniya ba zai kawo karshe ba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a ranar Talata cewa, Amurka za ta dakatar da kai hare-hare kan mayakan Houthi da ke da alaka da Iran a Yemen, yana mai cewa kungiyar da ke da alaka da Iran ta amince ta daina katse muhimman hanyoyin jiragen ruwa a Gabas ta Tsakiya.
Bayan da Trump ya bayyana hakan, Oman ta ce ta shiga tsakani kan yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma domin dakatar da kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka.
Ba a samu rahoton hare-haren Houthi kan jiragen ruwa a yankin tekun bahar maliya tun watan Janairu.
"Yarjejeniyar ba ta hada da Isra'ila ta kowace hanya, siffa ko tsari ba," Mohammed Abdulsalam, babban mai shiga tsakani na Houthi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.