Rikici tsakanin Pakistan da Indiya ya ɗau sabon salo
Sojojin Pakistan sun ce sun soma kai hare-haren ramuwar gayya akan Indiya, bayan sun zargi Delhi da kaddamar da munanan hare-haren makamai masu linzami a sansanonin sojojinta na sama guda uku.
India ba ta yi martani ba a kan wannan batu. Sai dai kasashen biyu na cigaba da zargin juna da ta'azzara rikici tun bayan hari da aka kai kan masu yawon-bude a yankin Kashmir a cikin watan da ya gabata.
Pakistan ta mayar da martani mai zafi tana mai jadadda cewa, a shirye take ta ce cas ga duk wanda ya fadamata kulle.
Wadannan su ne kalaman da sojojinta ke ambata bayan kaddamar da farmakin da suka bayyana da Operation Bunyanun Marsoos.
Kakakin sojojin ya ce sai sun tabbatar da cewa sun lalata kusan dukkanin sansanonin sojin saman kasar da India ke amfani dasu wajen kai mata hare-hare.
Sojojin Pakistan sun ce hare-haren India sun fada a depon ajiyar kayayyakin yaki, rumbun batira, da inda suke girke makaman artilary da hedikwatar manyan sojoji.
Yayin da wannan lamari ya sake dagula duk wani kokari na ganin an shawo kan rikicin tsakanin bangarorin biyu, Firaministan Pakistan ya kira taron gaggawa na kafatanin sojojin kasar, da kuma rundana ta musamman da ke kula da makaman nukiliyarta.
A wani taron manema labarai, mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka, Karoline Leavitt - ta ce washington na iya kokarinta wajen ganin an kawo karshen wannan rikici da ke neman zama gagarumin yaƙi.
"Wannan abu ne da sakataren harkokin waje, da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, Marco Rubio, ke ciki dumumu.
"Shugaban kasa ya nuna cewa yana son bangarorin biyu su mayar da wukakensu cikin gaggawa.
"Ya fahimci cewa dama kasashe ne da tun ba yau ba basa ga maciji da juna, tun kafin a san da shugaba Trump zai shiga ofis baa rasa kananan tashin-tashina.
"Sai dai kuma yana da kyakyawan alaka da shugabannin kasashen biyu, haka kuma sakataren harkokin waje, Marco Rubio, mun yi magana jiya.
"Kuma yana ta kokarin ganin an samu fahimtar juna da shugabannin kasahen biyu domin kawo karshen wannan rikici."
Kasashen nan mafiya karfin tattalin arziki a duniya wato G7 sun bukaci Pakistan da India su yi wa Allah su kai zuciya nesa domin kawo karshen wannan rikici.
Zaman tankiya tsakanin kasashen biyu ya tsananta ne tun bayan harin watan da ya gabata, inda India ke zargin Pakistan da mara baya da 'yan ta'adda da ke kai hari yankinta – zargin da Pakistan ta musanta.
Kasashen makwabtan juna, masu tinkaho da makaman nukiliyar da suka mallaka a tsawon gomman shekaru yankin Kashmir da ke karkashin ikon India yana fama da rikicin masu tayar da kayar baya – da ya lakume dubban rayuka.
Kuma Kowacce daga cikin kasashen biyu na ikirarin cewa yankin na Kashmir nata ne gaba daya.