Mayakan Houthi sun ce an kashe mutum hudu a hare-haren baya-bayan nan da Isra'ila ta kai a Yemen


Mayakan Houthi na Yaman a ranar Talata sun ce mutane hudu ne suka mutu kana wasu 39 suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama wanda ya biyo bayan harin makami mai linzami da mayakan da ke samun goyon bayan Iran suka kai kan babban filin jirgin saman Isra'ila.

Hare-haren na baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan yankin Houthi ya zo ne a daidai lokacin da rikicin yankin ke kara kamari kan shirin Isra’ila na fadada ayyukanta a Gaza tare da raba yawancin al’ummarta. da muhallin su

Tashar Talabijin ta Houthis ta Al-Masirah, ta nakalto ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce "An kashe 'yan kasar uku tare da jikkata wasu 35" a wata masana'antar siminti da ke Bajil, yayin da mutum daya ya mutu, hudu kuma suka jikkata a tashar ruwan Hodeida.

Mayakan Houthi dai sun zargi Amurka da Isra'ila da kai harin, amma yayin da Isra'ila ta tabbatar da kai harin, wani jami'in Amurka ya musanta hannun Amurka.

Harin na ranar Litinin ya zo ne bayan da wani makami mai linzami na Houthi ya kutsa kai a kewayen filin jirgin sama na Ben Gurion da ke kusa da Tel Aviv a karon farko, inda ya bar wani babban rami.

Mayakan  Houthi da ke iko da yankunan kasar Yemen, sun harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila da jiragen ruwa na tekun Red Sea a duk fadin yakin Gaza, suna masu cewa suna yin hadin gwiwa da Falasdinawa.

Isra'ila ta ce ta kai hari kan kasar Yemen sau biyar tun watan Yulin 2024, inda hukumomin Houthi suka bayar da rahoton cewa an kashe mutane 29.  Sojojin Isra'ila suna kame makamai masu linzami a kai a kai daga Yemen.

Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari tashar jiragen ruwa na Hodeida ne saboda ana amfani da ita wajen jigilar makamai da kayan aikin Iran, yayin da masana'antar siminti ta kasance "babban tushen tattalin arziki" ga mayakan.

Tun da farko a ranar Litinin, majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta amince da kara kai hare-hare a Gaza, ciki har da "mamaye" yankin.

 Mayakan Houthis sun dauki alhakin harin da aka kai a ranar Lahadin da ta gabata tare da yin barazanar sake harba makami mai linzami kan filayen jiragen saman Isra'ila.