Hamas ta ce ta gwabza kazamin fada da sojojin Isra'ila a Rafah na Gaza


Mayakan Hamas sun gwabza kazamin fada da sojojin Isra'ila a ranar Alhamis a kudancin zirin Gaza kusa da Rafah, in ji kungiyar Falasdinawa.

Sanarwar da aka fitar ta kafar Telegram ta nunar da cewa har yanzu Hamas na ci gaba da kai hare-hare a yankunan da sojojin Isra'ila suka fadada ikonsu, fiye da watanni 19 da fara yakin Isra'ila ta sama da ta kasa a Gaza

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce mayakan sun yi wa sojojin Isra'ila kwanton bauna a cikin wani gida a unguwar Tanur da ke yankin gabashin Rafah tare da wasu rokoki guda biyu na kakkabo makamai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji da dama.

Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga Isra'ila kan ikirarin Hamas.

Ba kasafai kungiyar ba ta bayar da rahoton fada a kusa da Rafah a 'yan watannin da suka gabata, inda aka ce mafi yawan tashe-tashen hankula a yankin gabas na birnin Khan Younis da ke kusa da yankin da kuma arewacin yankin gabar tekun.

Isra'ila ta ce a farkon wannan watan za ta kara tsawaita kai hare-hare a Gaza.

Isra'ila ta sake kai hare-hare a cikin Maris bayan rugujewar wata yarjejjeniya mai rauni, da Amurka ke marawa baya, wadda ta dakatar da fada na tsawon makonni shida.

Popular Posts