Faransa ta yi Allah wadai da shirin mamaye Gaza.
Ministan harkokin wajen Faransa ya fada a ranar Talata cewa "Paris" ta yi Allah wadai da sabon yakin da Isra'ila ta yi a zirin Gaza.
"Ba abin yarda ba ne," in ji Jean-Noel Barrot a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo, yana mai cewa gwamnatin Isra'ila "ta keta dokokin jin kai," bayan da majalisar ministocin tsaronta ta amince da wani shiri da wani jami'in Isra'ila ya ce zai haifar da "maye yankin Zirin Gaza da kuma rike yankunan.