'Yantawayen Syria na dab da kwace birni na uku kuma mafi girma a kasar
![]() |
A ranar Alhamis 'yantawayen Syria suka ayyana nasarar ƙwace birnin Hama |
Rahotanni daga Syria sun ce 'yantawayen tsaro na dab da shiga Homs, birni na uku mafi girma a Syria, a yayin da suke ci gaba da dannawa bayan birnin Hama a ranar Alhamis.
Dubban mutane ne ke tserewa daga birnin a yau Juma'a.
Wani jami'i a hukumar kula da 'yan gudun hijira a Syria da ya bar birnin Homs a safiyar yau ya ce ana cikin yanayi da kuma tserewa.
Mutane da dama sun tsere yayin da ƙalilan ɗin da suka rage kuma ke cikin damuwa, a duk lokacin da aka ji kara mutane na tsorata'', in ji shi.
Kwace birnin Homs zai rusa babbar hanyar da ke kai wa Damascus babban birnin hadarin.
Dakarun Syria sun ce sun kai wa matattarar 'yantawayen hari da jirage sama na samfur.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutum 300,000 sun rasa muhallansu a Syria tun bayan sake ɓarkewar edin basasar a makon daya gabata.