'Yan tawayen Syria sun ce sun ƙwace Damascus, kuma Assad ya tsere


 

Shugaban kungiyar 'yan tawayen da ke jagorar yakin da ake yi a Syria, ya ce mayakansa sun ƙwace babban birnin ƙasar, Damauscus.

Abu Mohammed al- Jawlani ya bayyana nasarar a matsayin abar tarihi, tare kuma da kira ga mayakansa da kada su cutar da duk wanda ya mika wuya.

Tun da farko 'yan tawayen sun ce sun kama birnin Homs, wanda shi ne birni na uku mafi girma a ƙasar.

Daman wani rahoton na cewa 'yan tawayen sun ce sun shiga babban birnin, Damascus, kuma Shugaba Bashar al-Assad ya tsere ba a san inda yake ba.

Kama birnin na Homs , wanda ya kasance birni na uku mafi girma a Syria, da 'yan tawayen na kungiyar HTS ( Hayat Tahrir al-Sham), suka yi babban koma-baya ne ga Shugaba Bashar Al-Assad, kasancewar hakan ya katse babban birnin kasar Damascus, daga sauran manyan sassan biranen kasar.

Tun da farko 'yan tawayen sun ce sun durfafi Damascus din daga bangarorin arewa da gabas da kudu – inda kuma ake ganin sojojin gwamnatin Syria kusan ba sa iya ko kuma ma a wasu wuraren ba sa son taka musu birki.

Homs ya kasance inda 'yan hamayya suke da karfi a farkon shekarun yakin basasar da aka fara a 2011.

Wani sashe na birnin ya kasance karkashin 'yan tawayen tsawon shekara uku, kafin daga baya gwamnati ta sake karbe iko da gaba daya birnin a karkashin wata yarjejeniya da majalisar dinkin duniya ta jagoranta a a 2014.

Yanzu dai ana ganin gwamnatin Assad na dab da faduwa, dan abin da ya rage mata na iko dan kadan ne, hasali ma ana cewa ba a san inda shugaban yake ba a yanzu.

Tuni ma wasu rahotanni ke cewa dakarun 'yan tawayen sun isa yankin wajen babban birnin inda suka kama gidan yarin Sednaya, wanda ya yi kaurin suna, kuma sun saki fursunoni.

Wasu mazauna birnin ma sun ce sun ji karar harbi a babban birnin.

Akwai ma rahotannin da ke cewa dakarun gwamnatin Syria sun tsere daga wasu wuraren da a da suka ja daga.

Har yanzu dai ba a san takamaimai ko mayakan 'yan tawayen za su ci gaba da dannawa ba tare da sun fuskanci tirjiya ba.

Tun da farko masu zanga-zanga a wajen babban birnin sun tumbuke mutum-mutumin marigayi mahaifin Shugaba Assad, Hafez, inda suka rika janshi a titi suka farfasa shi.

Wanda wannan wata alama ce ta nuna rashin jin dadi – abin da ba zai yuwu ba a 'yan kwanakin da suka gabata.

Wannan na nuna cewa ko a cikin babban birnin za a iya samun tawaye

Mutane da dama dai na murna da nasarar da suke samu.

To amma a kasa irin Syria wadda take rarrabe, ba za a yi saurin ayyana abin da zai kasance a gaba ba.

Ana ganin dai mutane da dama za su yi maraba da ganin karshen gwamnatin Assad – wanda yanzu a iya cewa dan lokaci ne kawai ya rage masa.

To amma abin tambaya a nan shi ne bayan gwamnatinsa sai me?

Domin dai kungiyar da ke jagorantar wannan galaba a kansa, HTS, tana da alaka da kungiyar Al Qaeda ne kuma tsawon shekaru suna ta kokarin nuna kansu a matsayin dakarun kishin kasa.

To amma mutane da dama ba su gamsu da su ba, suna cewa kungiya ce mai hadarin gaske, suna fargaba kan abin da zai iya kasancewa a gaba.

Popular Posts