Sharaa wanda aka fi sani da Abu Mohammed al-Jolani, shi ne ya jagoranci Hayat Tahrir al-Sham, ƙungiyar da ta tumbuƙe al-Assad a makon da ya gabata, lamarin da ya kawo ƙarshen shekaru 50 na mulkin wannan ahali.
Tuni Isra’ila ta shiga yankin da yarjejeniya ta haramta jibge sojoji da makami a cikin Syria, wanda aka samar bayan yaƙin da aka gwabza tsakanin Larabawa da Isra’ila a shekarar 1973.
Isra’ila wadda ta ce ba ta da niyyar dawwama a wannan yankin, ta bayyana kutsen nata a matsayin matakin wucin-gadi, don tabbatar tsaron kan iyaka, kuma ta kai ɗaruruwan hare-hare kan rumbunan ajiyar mahiman makamai na Syria.
A wata ganawa da wata tashar internet a Syria, Sharaa ya ce dalilan da Isra’ila ke bayarwa na aika-aikar da ta ke yi ba masu ƙarfi ba ne, yana mai cewa matakan da ta ke ɗauka na barazana ga zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Ya ƙarƙare da cewa tasirin da yaƙi ya yi kan Syria ba zai bari ta fara wani yaƙi ba, saboda abin da ta sanya a gaba shi ne kwanciyar hankali da sake gina ƙasar.