Me ya faru a Siriya? Ta yaya gomnatin al-Assad ta rushe?

Jama'a na murna a dandalin Umayyad da ke Damascus a ranar 8 ga Disamba, 2024


 

Da sanyin safiyar Lahadi ne dakarun adawa suka shelanta 'yantar da kasar Siriya daga mulkin shugaba Bashar al-Assad yayin da 'yan adawa suka kutsa cikin babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce tsohon shugaban da ake magana a kai ya fice daga Damascus, ba tare da wani bayani ba akan kasar da za ta tarbe shi.

An bayyana rugujewar Gomnatin kasar mai ban mamaki na fiye da shekaru 53 na mulkin al-Assad a matsayin wani lokaci mai cike da tarihi - kusan shekaru 14 bayan da 'yan Syria suka tashi a zanga-zangar lumana ta adawa da gwamnatin da ta gamu da su da tashin hankalin da ya rikide zuwa yakin basasa cikin sauri.

Mako guda da ya gabata, har yanzu gwamnatin na ci gaba da kula da wasu sassa na kasar. 

Popular Posts