Mbappe zai yi jinyar 'kwanaki 10', jinyarsa ta biyu a kakar bana


Wata sanarwa daga Real Madrid ta tabbatar da girman raunin da Kylian Mbappe ya samu a wasansu na ƙarshe da Atalanta a Gasar Zakarun Turai.

An maye gurbin Mbappe ne tun a zagayen farko na wasan da aka buga a gidan Atalanta, wanda Madrid ta lashe da ci 3-2.

A wannan wasan Mbappe ya samu nasarar zura ƙwallo ta farko tun a minti 10 da farawa, wanda ya ba shi damar cika jimillar ƙwallaye 50 a tsawon wasannin da ya buga a rayuwarsa a gasar ta Zakarun Turai.

Likitocin sun gano cewa Mbappe ya samu rauni ne a cinyarsa ta hagu a wasan da ya buga mintuna 35 kacal. Wannan ita ce jinya ta biyu da Mbappe ya tafi a kakar bana.

Bayan wasan, Carlo Ancelotti ya bagarar da batun raunin da Mbappe ya ji, inda ya ce ya cire shi ne da wuri sabola 'jijiyar ƙafarsa ba ta masa daɗi'. Sai a yanzu ne likitoci suka tabbatar da girman raunin nasa.

'Jinyar kwana 10'

Rahotannin na cewa tauraron ɗan wasan zai zai iya ƙauracewa filin wasa tsawon kwanaki 10, wanda ke nufin ba zai buga wasan Madrid na Asabar ba da Rayo Vallecano a gasar La Liga.

Sannan akwai barazanar Real Madrid za ta rasa ɗan wasan a wasan ƙarshe na gasar kofin nahiyoyi, Intercontinental Cup, wanda zai gudana a Qatar ranar 18 ga Disamba.

Yayin da Mbappe zai tafi jinya, masu sharhi na kallon batun a matsayin koma-baya ga koci Ancelotti wanda ke fama da rashin tabbas na yin nasara a wasa, a makonni bay-bayan nan..


Popular Posts