Kotun ƙolin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da ke neman a tsige shugaban Ƙasar, Bola Tinubu daga muƙaminsa.
Ƙarar wadda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Hope Democratic Party a zaɓen 2019, Ambrose Aworu, ya fitar tana neman kotu ta cire shugaba Tinubu a bisa zargin alaƙa da miyagun ƙwayoyi.
A hukuncin da suka bayar yau Litinin, alƙalan kotun suka bayar a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Uwani Abba-Aji sun yanke wa Mr Owuru tarar naira Miliyan biyar
Kotun ta kuma gargadi masu amsar ƙara kada su sake amsar ƙarar da bata da makama daga Mr Owuru.
A cikin ƙarar da ya shigar, Mr Owuru ya kuma yi zargin cewa shugaba Tinubu ɗan leƙen asiri ne na hukumar CIA ta Amurka, lamarin da ya haƙiƙance cewa ya saɓa wa sharaɗin zama shugaba ƙasa a Najeriya.