Kai-tsaye: Isra'ila ta yi luguden wuta a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza
Dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa bakwai, ciki har da wata mata da 'ya'yanta uku tare da jikkata gommai a hari ta sama da suka kai da sanyin safiya a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar kare fararen-hula ta yankin ta ce tawagarta ta gano gawawwakin mutanen bakwai a gidan iyalan "Khalifa" da ke sansanin na Nuseirat.
Wata majiya daga asibitin al-Awda ta ce an kai mutanen, ciki har da wata mata da 'ya'yanta, asbitin tare da waɗanda suka jikkata.
Kazalika harin na Isra'ila ya rusa gidan tare da lalata gidajen da ke maƙotaka, a cewar wasu ganau da suka yi hira da kamfanin labarai na Anadolu.