Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙarin mutum 37 a Gaza


Sojojin Isra'ila a safiyar yau sun kashe Falasdinawa akalla 37 a wasu hare-hare ta sama da suka kai kan masu gadi da ke rakiyar motocin agaji da kuma gidajen da suka kasance mafakar 'yan gudun hijira a yankin Gaza da yaki ya daidaita.

Wata majiyar lafiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Falasdinawa 15 ne suka mutu sannan wasu 30 suka jikkata a wasu hare-hare biyu da Isra'ila ta kai kan masu gadi da ke rakiyar motocin agaji a yankunan yammacin Rafah da Khan Younis da ke kudancin Gaza.

A tsakiyar Gaza, an kashe karin Falasdinawa 15 a wani hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wani gida da ke mafakar ‘yan kabilar Habbash a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, kamar yadda wata majiyar lafiya ta shaida wa Anadolu.

Wata majiyar lafiya ta kuma shaida wa Anadolu cewa Falasdinawa 7 ne suka mutu tare da jikkata wasu da suka hada da kananan yara a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gini a birnin Gaza.

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da ke bukatar tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza tare da bayyana goyon baya ga hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu da Isra’ila ke son haramta ayyukanta.

Kudirin Majalisar ba shi da amfani a bisa doka sai dai yana tasiri a ra’ayin duniya.

Isra'ila dai na fuskantar karin suka daga kasashen duniya kan yadda take gudanar da ayyukanta a Gaza musamman ma a batun agajin jin kai ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali a yankin da aka yi wa kawanya da kuma aka lalata.


Popular Posts