Isra'ila ta kai hari kudancin Lebanon da ya hallaka farar hula ɗaya

Rundunar sojojin Lebanon ta ce wani hari da Isra’ila ta kai yankin kudancin ƙasar ya raunata sojojinta huɗu da kuma hallaka farar hula ɗaya, duk da cewa har yanzu yarjajjeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Hezbullah da Isra’ila na ci gababa da aiki.


 A wata sanarwa da rundunar ta fitar a safiyar Litinin ɗin nan, ta ce Isra’ila ta yi amfani da jirgin saman yaƙi ne wajen kai hari kan wata mota a kan hanyar Saf al-Hawa a Bint Jbeil kusa da wani shingen binciken ababen hawa na sojoji, inda direban motar wanda farar hula ne ya rasa ransa.

Sojojin Isra'ila sun kai hari kan wata mota kusa da shingen binciken sojoji na Saf al-Hawa/Bint Jbeil, inda suka kashe wani farar hula tare da raunata sojojinmu hudu.

A ranar 27 ga watan daya gabata ne dai yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah ta fara aiki, duk da cewa dukkanin ɓangarorin sun sha zargin juna da saɓa mata.

Ko a ranar Litinin ɗin data gabata sai da sojojin Isra’ila suka kai wani hari kudancin Lebanon, da ma’aikatar kulada harkokin lafiyar ƙasar ta ce mutane 11 sun rasa ransu, wanda ke zuwa lokaci kaɗan bayan da mayaƙan Hezbollah suka yi iƙirarin kai harin farko cikin Isra'ila da ta ce sojanta ɗaya ya samu rauni bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Daga cikin sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da ɓangarorin biyu suka amince, akwai sashin da ya ce dukkanin ɓangaren Hezbollah da kuma Isra’ila za su janye sojojinsu daga kudancin ƙasar, tare barin sojojin Lebanon da na Majalisar Ɗinkin Duniya su ci gaba da kula da lamaransa.




Popular Posts