Gwamnan Kano ya cire sakataren gwamnati Baffa Bichi da kwamishinoni biyar

 

 

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da gyare-gyare a majalisar zartarwar jihar, inda ya cire wasu, sannan ya sauya wa wasu muƙamai.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya soke ofishin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, wanda Alhaji Shehu Wada Sagagi ke riƙwa, sannan ya sauke sakataren gwamnatin jihar, Dokta Baff Bichi saboda rashin lafiya.

Sanarwar ta ce gwamnan ya cire kwamishinoni guda biyar: Ibrahim Jibril Fagge na ma'aikatar kuɗi da Ladidi Ibrahim Garko ta ma'aikatar al'adu da yawon buɗe ido da Baba Halilu Dantiye na ma'aikatar watsa labarai da Shehu Aliyu Yammedi na ma'aikatar ayyuka na musamman da Abbas Sani Abbas na ma'aikatar raya karkara.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya yi sauye-sauyen ne domin inganta ayyukan gwamnati, da kai romon dimokuraɗiyya ga ƴanjihar.

Haka kum gwamnan ya yi wa wasu kwamishinonin sauyin ma'aiktu, waɗanda suka haɗa da: "mataimakin gwamnan jihar, wanda ak sauya masa ma'aikata daga ƙananan hukumomi zuwa ma'aikatar ilimi mai zurfi, da Mohammad Tajo Usman daga ma'aikatar kimiyya da fasaha zuwa ma'aikatar ƙananan hukumomi, da Dr Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata daga m'aikatar ilimi mai zurfi zuwa kimiyya da fasaha."

Sauran sun haɗa: "Hajiya Amina Abdullahi daga ma'aikatar jinƙai da rage talauci zuwa ma'aikatar mata, da Nasiru Sule Garo daga ma'aikatar muhalli da sauyin yanayi zuwa ma'aikatar ayyuka na musamman da Haruna Doguwa daga ma'aikatar ilimi zuwa ma'aikatar albarkatun ruwa."

Sai dai gwamnan ya buƙaci waɗanda aka cire ɗin su je ofishin gwamna domin a ba su wani aikin daban.


Popular Posts