Amurka da Isra'ila ne suka kitsa rushewar gwamnatin Assad - Iran
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya zargi Amurka da Isra'ila da kitsa kifar da gwamnatin Bashar al-Assad na Syria, yayin da ya kuma zargi wata "makwabciyar kasa" ta Siriya.
"Babu shakka cewa abin da ya faru a Siriya ya samo asali ne sakamakon wani makirci na hadin gwiwa tsakanin Amurka da sahyoniyawan," in ji Khamenei, yayin da yake magana kan faduwar al-Assad a karon farko a jawabin da ya gabatar a Tehran a ranar Laraba.
A cikin wani tsokaci da ya yi, Ayatollah ya kuma ce faɗuwar gwamnatin Assad ba za ta raunana ƙarfin Iran ba.
Ita kuwa Rasha ta bayyana kare lafiyar ƴan ƙasarta da ke Syria a matsayin "abu mai matuƙar muhimmanci", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar, TASS ya ruwaito.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Rasha, Maria Zakharova ta ce gwamnatin Rasha na tuntuɓar hukumomin Syria domin tabbatar da hakan.