Davies na son Madrid, Man Utd na kwadayin Dibling


 

 

Wakilin Alphonso Davies' ya nuna takacinsa kan yadda Bayern Munich ke tattauna batun sabon kwantiragin dan wasan Canada mai shekara 24 da yanzu haka ke son sauraron tayi daga Manchester United da Real Madrid. (Bild)

Mai yi wa Manchester City farauta ya gano mu su dan wasan Valencia daga Sifaniya Pepelu, mai shekara 26, da suke ganin shi yafi dacewa ya maye gurbin Rodri mai shekara 28 da ke jinya.(Football Transfers)

Dan wasan Southampton Tyler Dibling na cikin mutanen da Manchester United da Aston Villa ke farauta, matashin mai shekara ya kasance wadanda kungiyoyi har a Jamus da Italiya ke zawarci a yanzu.(Sun)

Da alama Crystal Palace ba za ta saurari tayin Manchester City da Arsenal kan dan wasanta na Ingila, Adam Wharton, mai shekara 20. (Football Insider)

Sabon kocin Leicester City Ruud van Nistelrooy na shirin gabatar da tayin daukan aron dan wasan Manchester United mai shekara 20, Toby Collyer. (Sun)

Celtic na iya daukan dan wasan Chelsea mai shekara 21 Carney Chukwuemeka a masatyin aro a watan Janairu. (Football Insider)

Barcelona ta shiga rububin dan wasa Jonathan Tah, da kwantiraginsa ke karewa Bayer Leverkusen a sabuwar kaka. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Barca na kuma bibbiyar dan wasan Sporting Viktor Gyokeres mai shekara 26, da wanda ke taka leda a Lille daga Canadian Jonathan David mai shekara 24, domin maye gurbin Robert Lewandowski, mai shekara 36. (AS - in Spanish)

Kocin Ipswich Kieran McKenna ya kasance mutumin da Tottenham ke hari a yanzu yayinda ake ganin yiwuwar ta kori kocinta, Ange Postecoglou. (Football Transfers)

Wani bincike ya nuna cewa Manchester City ta taba gabatar da tayin £35m a lokacin da Lionel Messi na Argentina ke Barcelona a bisa kuskure a 2008. (Star)


Popular Posts