Abin da aka zaɓe ta ta yi kenan
Jam'iyyar Conservative ta masu ra'ayin riƙau, ita ce ke adawa yanzu a Birtaniya bayan Labour ta doke ta a zaɓen da aka yi a watan Yulin 2024.
Daga cikin manyan manufofinta akwai ƙyamar baƙi da ke shiga ƙasar daga sassan duniya, waɗanda cikinsu akwai 'yan Najeriya da ƙasashen Afirka da dama.
An haifi Kemi a birnin Landan a shekarun 1980 kafin daga baya ta koma Legas, inda ta yi yarintarta. Ta koma Birtaniya daga baya inda ta zauna tare da ƙawar mahaifiyarta.
Naziru Mika'ilu tsohon babban editan jaridar Daily Trust ne a Najeriya kuma ɗalibi mai karatun digiri na uku a Birtaniya. Ya ce abin da Kemi ke yi na cikin aƙidun jam'iyyarta.
"Babu mamaki yanzu kalaman da mataimakin shugaban ƙasa ya yi su sa ɗan sassauta musamman kan abin da ya shafi Najeriya, saboda su ma 'yan jam'iyyarta ba za su so su alaƙanta kansu da abubuwan da take faɗa ba," a cewarsa.
"Amma dai matsayinta a kan baƙin haure da wasu abubuwa da suka shafi harkokin cikin gida ba za su sauya ba, saboda shi ne matsayin 'yan jam'iyyarta, waɗanda akasarinsu fararen fata ne masu ra'ayin riƙau.
"Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa masu goyon bayan jam'iyyarta suka zaɓe ta shi ne alƙwarin da ta yi na dawo da farin jininta, da kuma mayar da ita kan mulki. Saboda haka za ta ci gaba da yaɗa waɗannan manufofi."